Majiyoyin cikin gidan kasar Siriya sun watsa rahotonnin cewa: An ji fashe-fashen bama-bamai da wasu abubuwa da dama a cikin sansanin jiragen sama na “Kharab al-Jir” na Amurka da ke yankin arewacin jihar Hasakah na kasar Siriya, sakamakon wani hari da jirgi maras matuki ciki ya kai kan sansanin, inda wuta ta tashi tare da turnukewar hayaki a sararin samaniyar yankin.
A nashi bangaren, wani jami’in Amurka ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Reuters cewa: Wani jirgin yaki maras matuki ciki ne ya kai wa sansanin sojojin Amurka da ke Siriya hari, amma rahotannin farko sun nuna cewa ba a samu hasarar rai ba a sakamakon harin.
Jami’in ya kara da cewa: Rahotannin na farko ba su nuna an samu raunuka ba, amma likitoci suna ci gaba da tantance halin da ake ciki, kamar yadda ake gudanar da binciken irin barnar da harin yajanyo.
Tun daga ranar 19 ga watan Oktoban shekara ta 2023, an kai hare-hare har sau 135 kan sansanonin Amurka da aka kafa ba bisa ka’ida ba a cikin kasar Siriya.