Dakarun Sarayal-Quds bangaren sojin kungiyar Jihadul-Islami da kuma dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas sun tabbatar da cewa: Sun yi nasarar kashe sojojin mamayar Isra’ila tare da raunata wasu a farmakin hadin gwiwa da suka kai kan yankin “Unguwar Turawa” a kudu maso gabashin Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza.
Dakarun Sarayal-Quds a cikin wani takaitaccen bayani da suka fitar sun bayyana cewa: Sun gudanar da wani farmakin hadin gwiwa tare da dakarun Al-Qassam kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suka kutsa cikin yankin Unguwar Turawa a kudu maso gabashin Khan Yunus, bayan da suka yi artabu da su gaba da gaba.
A nata bangaren, rundunar Al-Qassam ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Mayakan Al-Qassam tare da mayakan Sarayal- Quds, sun samu nasarar kai hari kan sojojin yahudawan sahayoniyya da ke cikin wani gida, da makamai masu linzami na TBG.