Cibiyar Watsa Labaru ta Isra’ila don kare Hakkokin Dan Adam a cikin yankunan da aka mamaye, ta kira umarnin Isra’ila ga daukacin al’ummar Gaza na su fice daga yankin a matsayin ‘‘wauta’’.
A cikin wani sako da aka wallafa a shafukan sada zumunta, manyan kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce dole ne kasashen duniya su shiga tsakani a yanzu tare da “bukatar cewa Isra’ila ta dakatar da yakin nan take”.
“Bisa ayyukan Isra’ila, da alama tana da niyyar ci gaba da yaki har abada, da shuka ta’adi, da kuma kashe dimbin jama’a a nan gaba,” in ji kungiyar a jerin sakonni.
Jiya Laraba ne rundunar soji Isra’ila ta rarraba wasu takardun sanarwa da ke umartar Falasdinawa su fice daga birnin Gaza, wanda shi ne karo na biyu da ake umartar mutane su fice daga zirin, tun bayan fara yakin.
Takardun sanarwar sun yi gargadin cewa birnin ya kusa zama cibiyar gwabza yaki, tare da umurtar Falasdinawan su nufi biranen Zawaida da Deir al-Balah domin tsira.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tattaunawar tsagaita wuta wadda Amurka da Qatar da kuma Masar ke jagoranta, ko da yake
Amurka ta yi gargadin cewa har yanzu akwai gibi a tattaunawar.