Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Siriya ta sanar da cewa: Jami’an tsaron kasar da ke da alaka da gwamnatin rikon kwarya a kasar Siriya sun kai farmaki kan Masallata da ‘yan kasar ke gudanar da ibadu a cikin masallacin Al-Mustafa da ke unguwar Andalusia a garin Babila a cikin karkarar birnin Damascus, bayan da suka ki mika musu makullan masallacin da kuma rufe Masallacin saboda sabanin Mazhaba.
Hakazalika ‘yan daban Al-Jolani sun lalata ofisoshi da hotuna da ke cikin masallacin, lamarin da ya fusata mazauna birnin.
Masu lura da al’amura sun bayyana cewa: An gina masallacin ne da kudade daga mabiya Ahlul-baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su), kuma ba shi da alaka a hukumance da ma’aikatar kula da harkokin Baitul-Malin addini na kasar Siriya, wanda hakan na iya zama dalilin cece-kuce kan gudanar da masallacin.