Wata kungiyar farar hula ta kasar Spain “Caminando” ta bayyana cewa; An samu karuwar yawan mutanen da suke mutuwa akan hanyarsu ta zuwa Spain da kaso 58% a cikin shekarar 2024.
Jaridar “ Lo Figaro” ta kasar Faransa wacce ta nakalto alkaluman na kungiyar “Caminando”, ta kuma kara da cewa’ Idan za a raba wannan adadin a tsakanin ranaku, to a kowace rana ta Allah mutane 30 ne suke rasa rayuknsu, wanda kuma ya faru ne daga watan Janairu zuwa Disamba.
A tsakanin mutanen da su ka so yin hijira zuwa Spain da akwai mata 421 da kuma kananan yara da masu tasowa 1,538 da baki daya sun mutu.
Halina Malino wacce take kula da shirya wannan rahoton ta bayyana cewa; Abinda wannan adadin na wadanda su ka rasu yake nuni, shi ne cewa tsarin ceto da agaji baya aiki, kuma wannan wani bala’i ne da ba za a aminta da shi ba.
Kuma Malino ta yi kira da a bayar da muhimmanci ga hanyoyin kare rayuka, haka nan kuma ayyukan agaji da ceto.
Wadannan ‘yan ci-ranin dai sun fito ne daga kasashe 28 da mafi yawancinsu Afirka ne, sai kuma kasashen Iraki da Pakistan.