A jiya Jumma’a ce aka kammala taron kungiyar kasashen G20 a birnin johanasboug na kasar Afrika ta Kudu, kuma inda batun yake-yake a yankunan daban-daban na duniya ne suka mamaye taron.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yakin Ukraine da Rasha Hamas da HKI, Congo da sauransu ne suka mamaye taron inda ministocin harkokin wajen kasashen na G20 suka tattauna a kansu.
Ministan harkokin wajen na kasar Afrika ta Kudu Ronal Ramola ya bayyana cewa duk tare da cewa babu wani babban jami’an gwamnatin kasar Amurka a taron amma taron ya gudana kamar yadda ake saba.
Kungiyar G20 Taron kasashe masu arziki a duniya, wadanda suke da kasha 85% na tattalin arziki a duniya sannan suna da kasha 3/4 na harkokin kasuwanci a duniya.
Wannan ne karon farko wanda aka gudanar da taron a nahiyar afrrika, kuma a cikin watan Nuwamba na wannan shekaran ne za’a gudanar da taron shuwagabannin kasashen sannan Amurka ce zata karbi shugabancin kungiyar daga hannun afirka ta kudu.