Yahudawan Sahayoniya Suna Yin Hijirar Daga Haramtacciyar Kasar Isra’ila Zuwa Kasashen Waje

Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da

Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka.

Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu.

Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga  Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.

 Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20  da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can.

A cikin kafafen sadarwa na al’umma da akwai ‘yan share wuri zauna da dama da suke yin kira da a fice daga HKI zuwa kasashen Girka, Canada da Thailand domin ci gaba da rayuwa a can.

Batun yin hijirar ‘yan sahayoniya daga HKI ya fara ne tun farkon  farmakin Guguwar Aksa, da suke komawa zuwa kasashen turai mabanbanta bayan da su ka tabbatar da cewa, rayuwarsu ba za ta  dawwama ba a cikin kasar da su ka kwace daga masu ita na asali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments