A ci gaba da ayyukan tsokana da wuce gonad a iri, yahudawa masu tsattsauran ra’ayi sun kaddamar da farmaki kan yankunan Falastinawa da ke gabar yammacin kogin Jordan.
Yahudawa sun kashe wani Bafalasɗine tare da jikkata wasu uku a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, in ji Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu a hare-hare fiye da 1,270 da ‘yan ta’adda masu tsananin kishin kafa ƙasar Isra’ila suka ƙaddamar a kan Falasɗinawa tun watan Oktoban da ya gabata.
Sojojin Isra’ila da da Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun kashe Falasɗinawa aƙalla 680 sannan suka jikkata kusan 6,000 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Amurka da wasu kasashen Tarayyar Turai sun sanya takunkumai kan ‘yan kama-wuri-zauna masu tayar da hanklai sannan sun sha yin kira ga Isra’ila ta hana su kai hare-hare kan Falasɗinawa. Sai dai hakan bai hana ‘yan kama-wuri-zauna da masu kare su ci gaba da kashe Falasɗinawa ba.
Gwamnatin Isra’ila cike take da shugabannin Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna da kuma masu tsananin kishin kafa ƙasar Isra’ila, waɗanda suka kafa rundunar mayaƙan sa-kai a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Kudus.