WTO / IMF : harajin Trump, zai nakasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin duniya

Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) da asusun lamuni na duniya (IMF) sun nuna damuwa game da tabarbarewar tattalin arziki daga sabbin harajin da gwamnatin Trump

Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) da asusun lamuni na duniya (IMF) sun nuna damuwa game da tabarbarewar tattalin arziki daga sabbin harajin da gwamnatin Trump ta laftawa duniya, suna masu gargadin cewa hakan zai iya kawo cikas ga harkokin kasuwanci da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, WTO ta yi hasashen cewa harajin Amurka da ya hada da wanda aka gabatar a farkon wannan shekara zai iya rage cinikin hajoji a duniya da kashi 1 cikin 100 a shekarar 2025, wanda zai kaucewa hasashen da ta yi a baya na fadada cinikayya.

Rahoton ciniki na duniya na WTO, wanda aka fitar a watan Oktoban bara, ya yi hasashen cinikin kayayyaki a duniya zai karu da kashi 3 cikin 100 a bana, saidai karuwar rikicin siyasa da rashin tabbas kan manufofin tattalin arziki a yanzu sun sanya shakku sosai kan wannan hasashen.

Darakta-Janar na WTO Ngozi Okonjo-Iweala ta yi gargadin cewa matakan harajin na iya rikidewa zuwa yakin cinikayya, wanda zai kai ga daukar matakin ramuwar gayya daga wasu kasashe da kuma kara cutar da kasuwancin duniya.

Ita ma a nata bangaren, shugabar hukumar ba da lamuni ta duniya IMF, Kristalina Georgieva, ta bayyana irin wannan damuwar a ranar Alhamis, inda ta bayyana irin hadarin da harajin na Amurka ke haifarwa ga daidaiton tattalin arzikin duniya.

Yayin da IMF ke ci gaba da tantance tasirin lamarin, ta yi gargadin cewa wadannan matakan za su iya dagula hasashen ci gaban da aka samu a duniya da kuma haifar da rashin tabbas.

Sabon harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a baya-bayan nan, wanda zai fara aiki a ranar Asabar, ya sanya kashi 10% kan duk wasu kayayyakin da ake shigowa da su kasar waje, tare da karin haraji kan kasashen da ke da gibin kasuwanci mafi girma da kasarsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments