Jaridar Wall Street Jouranl ta kasar Amurka ta buga labarin da yake cewa, kasar Amurka ta fara girke makamai a kusa da tekun Caribbean da kuma wasu jiragen sama a arewacin kasar Venezuela.
Labarin ya kara da cewa;Rundunar da ma’aikatar yakin Amurka ta “Pentagon” ta girke ta zaratan mayakan kundunbala ce wacce ta kashe Usama Bin Ladan a kasar Pakistan.
Wani sashe na rundunar ya hada jirage masu saukar Angulu da ake iya amfani da su wajen kai hari.
A cikin kwanakin bayan nan dai Amurka ta kara matsin lamba akan kasar Venezuela ta hanyar kai wa jiragen ruwan da suke fitowa daga kasar hare-hare, bisa zargin cewa suna dauke da muggan kwayoyi zuwa Amurka.
Gwamnatin Venezuela da kasashen yankin masu kin jinin danniyar Amurka sun yi watsi da zargi tare da bayyana shi a matsayin wani sabon yunkuri na sake dawo da yake-yaken da Amurka ta yi a cikin wannan yankin na Caribbean a shekarun baya.