Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana damuwa kan yaduwar sabon nau’in cutar kyandar biri, da yanzu haka ke saurin yaduwa a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo.
Mista Tedros Adhanom ya tabbatar da cewa zai karbi shawara a yau don ganin ko za a ayyana cutar a matsayin mai matukar hadari a fadin duniya.
Cikin jawabin da ya gabatar a farkon taron gaggawa da Hukumar ta yi, ya ce a shekarar da ta gabata an samu karuwar wadanda cutar ta kama, sannan kuma yawan wadanda suka kamu a shekarar da muke ciki ma ya zarta na bara da dubu 14, sannan an samu mace-mace 524.
Dr Tedros, ya ce a watan daya wuce kadai an samu wadanda suka kamu da sabuwar nau’in cutar a kasashe kamar Burundi da Kenya da Rwanda da kuma Uganda, inda a bara ba a samu bullar cutar ba.
Hukumar Lafiya ta Duniyar ta fara shirin daukar mataki kan cutar a nahiyar Afirka, inda take bukatar dala miliyan 15 domin lura da yaduwa da kuma shiryawa cutar.