Search
Close this search box.

WHO Na Da Niyyar Yi Wa Yara 600,000 Allurar Rigakafin Cutar Shan Inna A Gaza

Hukumar Lafiya Ta Duniya, ta yunkuri anniyar aikewa da alluran riga kafi na cutar shan inna ko kuma Polio a zirin Gaza. Shugaban hukumar ta

Hukumar Lafiya Ta Duniya, ta yunkuri anniyar aikewa da alluran riga kafi na cutar shan inna ko kuma Polio a zirin Gaza.

Shugaban hukumar ta WHO, ya ce hukumarsa na aikewa da allurar rigakafin cutar shan inna fiye da miliyan daya zuwa zirin.

Za a yi allurar rigakafin a cikin makonni masu zuwa ga yara 600,000 ‘yan kasa da shekaru takwas.

“Gano cutar ta polio da akayi a cikin ruwa mai daskarewa a Gaza wata alama ce da ke nuna cewa cutar tana yaduwa a cikin al’umma, kuma hadari ne ga yaran da ba a yi musu allurer ba,” in ji shugaban na WHO a wani sakon da ya wallafa a shafin X.

“Muna bukatar cikakken ‘yancin tafiye-tafiye na ma’aikatan kiwon lafiya da kayan aikin likita don gudanar da wadannan ayyuka cikin aminci da inganci,” in ji shi.

“Ana bukatar tsagaita wuta, ko ‘kwanaki na kwanciyar hankali’ yayin shirye-shiryen da gudanar da kamfen din rigakafin, don kare yara a Gaza daga cutar ta shan inna.” Inji Shugaban hukumar ta WHO.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments