Welayati: Makircin Amurka da Isra’ila na kwance damarar Hizbullah ba zai yi nasara ba

Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci


Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu.

Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon.

“Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi.

Ya yi ishara da matakan siyasa da wasu bangarori na Labanon suke dauka da nufin kwance damarar Hizbullah, yana mai bayyana su a matsayin wadanda suka tasirantu da matsin lamba daga Amurka da Isra’ila.

Velayati ya ce Washington da “Isra’ila” sun yi imanin za su iya maimaita wani yanayi irin na kasar Syria a Lebanon, inda suka yi amfani da Jaulani domin aiwatar da wanan manufa, amma wannan  mafarkin ba zai zama gaskiya ba, kuma Lebanon kamar kullum, za ta ci gaba da zama mai gwagwarmaya domin rayuwa a cikin martaba da karama.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted