Wata Kutu A Nan Iran Ta Yanke Hukuncin Tarar Dalar Amurka Biliyon $4 Kan Gwamnatin Amurka Saboda Tallafawa Ayyukan Ta’addanci

Wata kutu a nan Tehran ta yanke hukuncin tara wanda ya kai dalar Amurka biliyon 4.130 kan gwamnatin kasar Amurka wacce ta tabbatar da hannunta

Wata kutu a nan Tehran ta yanke hukuncin tara wanda ya kai dalar Amurka biliyon 4.130 kan gwamnatin kasar Amurka wacce ta tabbatar da hannunta a hare haren ta’addancin wanda kungiyar yanta’adda Jundullah ta kai kan wasu wurare a gundumar Pishin na lardin Sitan Baluchestan a ranar 8 ga watan Octoban shekara ta 2009.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin kotu, mai lamba 55Th karkashin ma’aikatar shariar kasar, kuma kotun shari’o’in kasa da kasa tana wannan bayanin.

Labarin ya kara da cewa a hare-haren ranar 8 ga watan Octoban shekara ta 2009 dai, mutane 45 ne suka rasa rayukansu a yayinda wasu 57 suka ji rauni. Kuma mutane 142 ne suka bada shaida kan yadda hare haren ta’addancin suka kasance.

Labarin ya kara da cewa daga baya gwamnatin kasar Iran ta kama shugaban kungiyar yanta’addan Abdulmalik Riki a lokacinda yake kan hanyarsa ta zuwa wani sansanin sojojin Amurka a kasashen tsakiyar Asiya.

Sannan a binciken da aka yi masa ya bada shaidu wadanda suka tabbatar da cewa gwamnatin kasar Amurka ce ta samar da kungiyar take kuma bata duk abubuwan da take bukata don aikata ayyukan ta’addanci a cikin kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments