Wata Kotu a Canada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci

Wata kotun tarayya a kasar Canada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon

Wata kotun tarayya a kasar Canada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun.

Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan Yunin 2025, ta hana dan siyasar izinin shiga kasar bayan samun shi da gaza cika sharudan dokar shige da fice ta kasar.

A cewar alkalin, “Dabi’ar wasu ’yan siyasa ’yan PDP, wadanda wasu daga cikinsu ma kusoshi ne a jam’iyyar, da wadanda suka aikata laifukan siyasa ko aka yi da yawunsu, ta yi yawan da ba zai yiwu a ki alakanta shugabancin jam’iyyun da ita ba.”

Ana sa ran dai nan ba da jimawa ba gwamnatin Najeriya za ta fitar da sanarwa kan matsayinta a hukumance, kamar yadda wani babban jami’in gwamnati ya tabbatar mana, yana mai bayyana hukuncin a matsayin abin takaici.

Ita kuwa jam’iyyar PDP, ta bakin mamba a kwamitinta na zartarwa, Timothy Osadolor, ta ce kotun na da ’yancin fadin albarkacin bakinta, amma hukuncin nata ba yak an gaskiya.

“Amma babu wata hujja a cikin ra’ayin nasu da zai sa dukkan abin da suka fada a cikin hukuncin nasu ya zama gaskiya,” in ji Timothy.

Ya ce a maimakon ayyana jam’iyya gaba dayanta a matsayin kungiyar ta’addanci, kamata ya yi kotun ta fadi sunan masu alaka da ta’addancin kai tsaye, musamman a cikin jam’aiyyar APC.

Ya kuma bayyana hukuncin a matsayin na yanke kauna da salon shugabancin gwamnatin Najeriya a karkashin Shugaba Bola Tinubu, inda ya bukaci gwamnatin da kada ta dauki lamarin da wasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted