Wata Kotu A Iran Ta Ci Taran  Gwamnatin Amurka Dala Biliyon $12.6 Saboda Cutar Da Masu Fama Da Cutar ‘thalassemia’ A Kasar

Wata koto a nan Tehran ta ci gwamnatin Amurka taran dalar Amurka biliyon $12.6 saboda hana wadanda suke fama da cutar ‘Talamessia” a kasar. Tashar

Wata Kotu A Iran Ta Ci Taran  Gwamnatin Amurka Dala Biliyon $12.6 Saboda Haddasa Mutuwar Masu Fama Da Cutar 'thalassemia' A Kasar

Wata koto a nan Tehran ta ci gwamnatin Amurka taran dalar Amurka biliyon $12.6 saboda hana wadanda suke fama da cutar ‘Talamessia” a kasar.

Tashar talabijin ta Presstv  a nan Tehran ta ce a shekara ta 2018 ne gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar sannan ta dorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, wanda ya hada da magungunan cutar Talassemia.

Labarin ya kara da cewa Kotu mai lamba 55 wanda yake kula da kararraki na kasa da kasa a jiya Laraba ta yanke hukun kan wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suke da hannun kasi tsaye na wajen dorawa kasar takunkuman tattalin arziki har da magungun wannan cutar.

Kafin haka dai masu fama da wannan cutar  thalassemia 438 ne suka shigar da kara kan mutane 17 na gwamnatin Amurka wadanda suke da hannu wajen aiwatar da takunkuman tattalin arziki na magunguna a Amurka.

Kotun ta yanke hukuncin tarar ne a kan wadanda Jami’an gwamnatin Amurka, wadanda suka hada da wadanda cutar ta gurgunta, ko ta yi masu wata illa. Ko barna ga masu mafa da cutar. Magungunar cutar Thalassemia masu kyau dai ana samunsu a kasar Amurka ne. Rashin samunsu ya tilastawa wasu amfani da jabun magani daga wasu kasashen wanda hakan ya kara yawan kudaden da suke kashewa cutar.. Takunkuman tattalin arzikin sun gurgunta ko sun jawo mutuwar mutane da dama a kasar Iran don haka wannan tarar ta dace da irin wannan laifin

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments