Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da kwashe wasu sojoji 200 daga wani sansanin soji da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye sakamakon wata gobara da ta tashi a kusa da wajen.
Shafin yada labarai na Isra’ila Ynet ya bayar da rahoton cewa, rundunar sojin ta kwashe dakarun daga wani sansani da ke kusa da kudancin Kfar Etzion yayin da gobara ta tashi a wani budadden wuri da ke kusa da sansanin.
Sai dai rundunar sojin ba ta faɗi abin da ya tayar da gobarar ba.
Shafin intanet ɗin ya ƙara da cewa an aika tawagar ‘yan kwana-kwana 20 da jirage shida don ƙoƙarin shawo kan gobarar.
Kfar Etzion wani matsugunin Isra’ila ne da aka gina a kasar Falasdinu a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.
A karkashin dokokin kasa da kasa, ana daukar duk matsugunan Yahudawa a yankunan da aka mamaye.