Kotun kare kundin tsarin mulki a kasar Korea ta Kudu ta tabbatar da tsige shugaban kasa Yoon Suk Yeol daga kan kujerar shugabancin kasar a safiyar yau Jumma.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalan kotun koli na kare kundin tsarin mulkin kasar, su 6 suna karanta wannan hukuncin da suka yanke kan tsahoin shugaban.
Kafin haka dai Yeol lauya ne wanda ya shiga harkokin siyasa a yan shekarun da suka gabata, sannan ba zata ya lashe zaben zama shugaba a shekara ta 2022. Amma a shekarar da ta gabata wato 2024 ya kafa doka t abaci a kasar saboda kare kansa da matarsa daga wasu kura kurai da suka aikata. Wannan dokar day a kafa ya rikita harkokin siyasa a kasar na wani lokaci.
Wanda ya kai ga majalisar dokokin kasar ta tubeshi daga kan kujerar shugabancin kasar. Amma daya baya kotun kundin tsarin mulkin kasar ta dauki alhakin duba cikin lamarin. Inda daga karshe ta tabbatar da tube shi a safiyar yau Juma’a.
Kafin haka dai a jibge jami’an tsaro kan manya-manyan titunan birnin seoul don hana duk wani tashin hankali dangane da hukuncin da kotun zata yanke.