Wata tashar talabijan ta Larabci ta bada labarin cewa, wasu yan bindiga sun shiga ofishin jakadancin JMI dake birnin Damascus babbabn birnin kasar Siriya a jiya Lahadi,, inda suka lalata kayakin aikin da suke cikinsa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto tashar talabijin ta Al-Arabiyya ta kasar Saudiyya ta na watsa wasu hotunan bidiyo wadansa suka nuna cikin ofishin jakadancin kasar ta Iran a birnin Damascas babban birnin kasar Siriya da kuma yadda aka lalata kayakin da suke cikinsa.
Labarin ya kara da cewa jim kadan bayan shigowar yan tawaye na Hai’at Tahrirusham birnin Damaus ne, hakan ya faru. Kafin hakan dai, sojojin kasar ta Siriya sun bada sanarwan faduwar gwamnatin shugaba Al-Asad.
Har’ila yau mayakan ‘Hai’at Tahrirusham’ sun kutsa cikin fadar shugaban kasa a Damascus da kuma wasu manya-manyan cibiyoyi da ofisoshin gwamnati a birnin. Shugaba Al-Asad dai ya bar kasar kafin shigowar mayakan na HTSH, da jirgin sama na kasar Rasha, kuma jirgin ya bi ta kan birnin Khums na kasar ta siriya kafin a daina ganinsa daga cikin rada.