Search
Close this search box.

Wasu Mata Uku Da Karamin Yaro Sun Yi Shahada Sakamakon Harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Wasu mata Falasdinawa uku da wani yaro daya sun yi shahada sakamakon harin bam da yahudawan sahayoniyya suka kai a Gaza Majiyoyin cikin gida a

Wasu mata Falasdinawa uku da wani yaro daya sun yi shahada sakamakon harin bam da yahudawan sahayoniyya suka kai a Gaza

Majiyoyin cikin gida a Falasdinu sun watsa rahoton cewa: Wasu mata guda uku da wani karamin yaro sun yi shahada sakamakon luguden bama-bamai da jirgin saman yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi kan wani gida na iyalan Al-Bakri da ke yammacin birnin Gaza.

Sannan wasu jiragen saman yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare kan yankin kudu maso gabashin unguwar Al-Zaytoun dake gabashin birnin Gaza, da kuma wani farmaki a kofar shiga sansanin Bureij da ke tsakiyar zirin Gaza.

Kamar yadda sojojin mamayar na yahudawan sahayuniyya suke ci gaba da aikata muggan laifukan kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 252 a jere, ta hanyar kai hare-hare da dama ta sama da kuma harba makaman roka, a yayin da suke aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula, a daidai lokacin da ake cikin wani mummunan yanayi na jin kai sakamakon kawanya da suka yi wa yankin kuma yawan ‘yan gudun hijirar sun kai sama da kashi 95% na al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments