An kashe wani kusa a kungiyar Hamas Hassan Farhat, wanda aka fi sani da Abu Yasser, da wasu mutane biyu a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai a wani gida a birnin Sidon, dake kudancin kasar Lebanon, a safiyar jiya Juma’a.
A cewar Al-Mayadeen, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai wani hari ta sama kan wani gida da ke birnin Sidon da ke kudancin kasar Lebanon, inda harin ya kashe babban kusa na Hamas Hassan Farhat da wasu mutane biyu daga cikin iyalansa.
A cewar rahoton, sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari a Al-Naqoura, Nabatiyeh, da Sidon a kudancin kasar Lebanon a yammacin ranar Alhamis, inda suka yi barna a yankunan da aka kai harin.
Shafin tashar “Russia Today” ya bayar da labarin cewa: Bisa kididdigar farko da aka yi, “Hassan Farhat, wanda aka fi sani da Abu Yasser”, shugaban kusa a kungiyar Hamas, da dansa da ‘yarsa ne suka yi shahada a wani hari da jiragen Isra’ila suka kai a wani gida a yankin Dala’a a tsakiyar garin na Sidon. A wannan harin da aka kai ta hanyar amfani da jirgi maras matuki, an harba makamai masu linzami guda biyu a gidan.
Kawo yanzu kungiyar Hamas ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da shahadar Farhat ba, inda ta jaddada matsayinta na ci gaba da bin tafarkin neman ‘yanci wanda Farhat da iyalansa suka yi shahada a kansa.
Dangane da haka ne ma’aikatar lafiya ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu wasu biyu kuma suka jikkata sakamakon wannan hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a birnin da ke kudancin kasar Lebanon.