Wani Jirgin Amurka Samfurin F-18 Na 3 Ya Fadi A Tekun “Red-Sea”

  Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon

  Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”.

Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka akan doron jirgin ruwan dakon jiragen saman na ” USS Harry Trauman”.

Sanarwar ta kuma kara da cewa; Matuka jirgin sun fice daga cikinsa ta hanar lema, kuma an tserato da su daga cikin ruwa ta hanyar jirgi mai saukar angulu. Matukan, kamar yadda sanarwar ta sojojin na Amurka, sun ji rauni.

Wani jami’in soja wanda ya bukaci a sakaya sunansa  ya fada wata kafar watsa labaru cewa; Yawan faduwar da jiragen yakin samfurin F-18 suke yi, ya ja hankalin manyan kwamandojin sojan Amurka.”

A  ranar 28 ga watan Afrilu ma dai rundunar sojan ruwan Amurkan ta sanar da faduwar  jirigin yakin samfurin F-18 a lokacin da yake sauka.

Bugu da kari a cikin watan  Disamba na shekarar da ta wuce, wani jirgin saman ya fado ya ci karo da jirgin dakon jiragen yakin kamar yadda rundunar sojan ruwan Amurkan ta sanar.

Wasu masu bin diddigin abinda yake faruwa a yankin suna danganta fadowar jiragen saman na Amurka da hare-haren kungiyar Ansarullah ta Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments