Dakarun Yeman ta sanar cewa ta kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Isra’ila, a wani mataki na nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da ke fama dake fusnkatar mamaya, zalinci da kisan kare dangi daga Isra’ila.
Kakakin rundunar sojin Isra’ila ya ba da rahoton wani sabon hari da makami mai linzami daga Yeman, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa zuwa matsuguni.
Rundunar ta ce ta kunna na’urar tsaronta ta sama domin tinkarar barazanar, amma ta kasa dakile makamin.
Tun ma kafin sanarwar da sojojin Isra’ila suka fitar, kafofin yada labaran Isra’ila sun ba da rahoton kararrakin gargadin makamai masu linzami a yankuna da dama na tsakiyar Falasdinu da ta mamaye.
Daga baya an sanar da cewa an dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen da ke zuwa filin jirgin Ben Gurion.