A wani rahoto da jaridar ta buga ta bayyana cewa; Kudaden fito da shugaban kasar Amurka ya kara, da kuma kame ‘yan hijira da ake yi, sun fara nuna mummunan sakamako.
Jaridar ta ce an fara ganin sakamakon matakan na Shugaba Trump ne a cikin rayuwar Amurka saboda yadda kayan da suke saya a cikin shaguna su ka kara kudi. Haka nan kuma ana samun koma baya wajen karuwar ayyukan yi saboda siyasa mai tsauri akan ‘yan hijira.
Wani sashe na rahoton ya ce, duk da cewa tattalin arzikin Amurka din ya nuna juriya akan yakin tattalin arzikin da Donald Trump ya shelanta, amma sauraron ra’ayin jama’a ya nuna cewa tasirin hakan zai bayyana ta yadda za a ji shi a jiki.
Tun bayan shigarsa fadar mulkin Amurka a farkon wannan shekara Donald Trump ya fito da siyasar kara kudaden fito akan hajar kasashe abokan kasuwancin kasarsa. Wasu daga cikin wadannan kasashen sun mayar da martani ta hanyar dorawa hajar Amurkan takunkumi.