Wakilin Jagoran Juyi A Wurin Jana’izar Sayyid: Gwgawarmaya Za Ta Ci Gaba

Wanda ya wakilci jagoran juyin juya halin musulunci na Iran a wajen jana’izar Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah da kuma Shahid Safiyuddin Hashim,

Wanda ya wakilci jagoran juyin juya halin musulunci na Iran a wajen jana’izar Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah da kuma Shahid Safiyuddin Hashim, ya gabatar da jawabi da a ciki ya bayyana cewa: Jagoran jihadi mai girma, kuma shugaban gwgawarmaya a cikin wannan yankin, Sayyid Hassan Nasrallah ( Allah ya daukaka matsayinsa)  ya kai matsayi na koli na daukaka da izza.

Sayyid Mujtaba al-Husainy ya kuma ce; A wannan lokacin za a binne gangar jikin Sayyid a cikin kasar da ya yi jihadi saboda Allah akanta, amma ruhinsa da kuma tafarkinsa na gwgararmaya zai kara daukaka fiye da kowane lokaci a baya.

Sayyid Mujtaba al-Husaini ya kuma ce:Makiya su kwana da sanin cewa, gwgawarmaya za ta cigaba da wanzuwa domin fuskantar zalunci da girman kai na duniya, ba kuma za ta karaya ba har sai an cimma manufa, da izinin Allah.”

Da yake Magana akan Sayyid Hashim Safiyuddin ( Yardar Allah a gare shi) ya bayyana shi a matsayin wani daga cikin taurari masu haske a cikin tarihin wannan yankin. Ya kuma kasance mataimaki mai tsarkin zuciya ga Sayyid Hassan Nasrallah.

A karshe Sayyid  Mujtaba al-Husaini ya yi addu’a ga wadannan shahidan biyu masu  girma da kuma sauran mujahidai da  dukkanin shahidai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments