Wakilin Amurka na musamman ya ziyarci Sudan tare da jaddada bukatar Amurka na ganin an kawo karshen yaki a kasar
Kimanin watanni 9 da nada shi a matsayin wakilin Amurka a Sudan, Tom Perriello, ya ziyarci Sudan tare da gudanar da zaman tattaunawa da shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin kasar karkashin gwamnatin rikon kwarya Janar Abdul-Fattah Al-Burhan.
Bangarorin biyu sun gudanar da shawarwari ne a birnin Port Sudan a ziyarar jami’in na Amurka ta farko a kasar, Periello ya tattauna da Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki, Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa Malik Agar da Ministan Harkokin Waje Ali Youssef, da shugaban kabilar Masalit, Sa’ad Bahr al-Din, da kuma wakilan kungiyoyin fararen hula da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, inda suka tattauna game da yanayin ayyukan jin kai, neman hanyar dakatar da yaki a kasar, da kuma batun gudanar da tsarin siyasa.
Tun a watan Agustan da ya gabata ne aka shirya Periello zai kai Ziyara zuwa birnin Port Sudan, amma a kan sharadin zai gana da jami’an Sudan ne a filin jirgin saman birnin, saboda abin da aka kira kudurin tabbatar da tsaro saboda rashin ofishin jakadancin Amurka a Sudan, amma majalisar gudanar da mulkin Sudan ta ki amincewa da hakan.