Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya sanya hannu kan dokar kafa cikakkiyar rundunar tsaro ta kasa a wannan Laraba.
Maduro ya jaddada bukatar kafa cikakkiyar rundunar tsaro, wacce ta hada dukkan cibiyoyin soja na gwamnati da kuma dakarun sa kai najama’a a safiyar yau Laraba.
Dokar na da nufin tsara da kuma hada dukkan cibiyoyin gwamnati, kamar sojoji da ‘yan sanda, da kuma al’umma wajen fuskar barazanar waje ko ta ciki, a karkashin ka’idar kare cikakken tsaro” na Venezuela daga duk wata barazana ga kasar.
Mahimmancin wannan doka ya ta’allaka ne kan karfafa ikon shugaban kasa da na sojoji a cikin mawuyacin hali. Yana nuna yanayin da ake ciki na mayar da hankali kan ayyukan soja ga gwamnati da al’umma, kuma ana amfani da hakan a siyasance don karfafa ikon kasa wajen fuskar adawa da takunkumin kasa da kasa.
A wani ci gaba makamancin haka, Shugaban Colombia Gustavo Petro shi ma ya ba da umarnin dakatar da musayar bayanan sirri da Amurka a wannan Laraba.
Kimanin mako guda da ya gabata, shugaban Venezuela ya amince da shawarwarin Jam’iyyar Hadin Kan Gurguzu taLatin Amurka na komawa ga gwagwarmayar mamakami idan aka samu wani hari daga Amurka a kan kasar, bisa la’akari da jibge sojojin ruwa da Amurka ta yi a cikin yankin Caribbean.