Vatican: Yakin Isra’ila a Gaza yaki ne a kan mutane raunana marasa kariya

Sakataren harkokin wajen Vatican, Cardinal Pietro Parolin, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa, “yakin da sojojin Isra’ila suke yi a yankin

Sakataren harkokin wajen Vatican, Cardinal Pietro Parolin, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa, “yakin da sojojin Isra’ila suke yi a yankin zirin Gaza yaki ne a kan mutane raunana marasa kariya.”

Cardinal Parolin ya yi ishara da cewa “dole ne kasashen duniya su nuna shakku kan sahihancin ci gaba da samar da makamai  wadanda ake amfani da su kan fararen hula a Gaza.”

A lokuta da dama Paparoma Leo na 14 ya yi Allah wadai da yakin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza, yana mai yin kira da babbar murya  ga kasashen duniya da su kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, wanda aka kwashe kusan shekaru biyu ana yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted