Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu (UNRWA) ya yi maraba” da kuri’ar Majalisar Dinkin Duniya na neman ra’ayin kotun kasa da kasa (ICJ) game da wajabta wa Isra’ila saukaka hanyoyin samar da kayan agaji zuwa Gaza.
Yunkurin da Isra’ila ta yi na haramta UNRWA zai hana Falasdinawa samun “taimako na ceton rai” da kuma ‘yancin samun ilimi ga dubban daruruwan Palasdinawa yara a Gaza in ji shi.
“Dole ne a kiyaye mutunta dokokin kasa da kasa ba tare da ware wasu ba,” in ji shi.
A jiya ne Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar neman Kotun Duniya ta ICJ ta bayyana ra’ayinta kan wajibcin da ke kan Isra’ila wajen ganin an isar da agajin da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa ciki har da MDD ke bayar wa ga Falasdinawa
Majalisar mai wakilai 193 ta amince da kudurin da Norway ta tsara, inda kasashe 137 suka kada kuri’ar amincewa.
Isra’ila da Amurka da wasu kasashe 10 sun kada kuri’ar rashin amince wa da shi, yayin da kasashe 22 suka kaurace.
Matakin dai ya zo ne a matsayin martani ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da ayyukan Hukumar Kula da ‘Yan gudun Hijira ta MDD ga Falasdinu UNRWA a kasar daga karshen watan Janairu.