Kwamandan dakarun MDD dake kasar Lebanon ya bayyana cewa; Matukar ana son a aiwatar da kudurin MDD mai lamba 1701 kamar yadda yake, ya zama wajibi a kare hurumin kasar Lebanon.
Kwamandan Dakarun Majalisar Dinkin Duniyar a Lebanon Manjo Janar Diodato Abagnara wanda ya gabatar da jawabi a lokacin da ake bikin cikar kasar Lebanon shekaru 88 da samun ‘yanci, ya kara da cewa; Sojojin kasar Lebanon abokan aikinsu ne wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Kudancin Lebanon.”
Har ila yau ya bayyana cewa, shigar sojojin kasar Lebanon a dukkanin yankunan kudancin kasar yana da daga cikin muhimman yunkuri na shimfida ikon gwamnati a fadin kasar.
A gefe daya kwamandan sojan kasar Lebanon Rodoulf Haykal ya bayyana cewa, kasar tana cikin wani yanayi na ayyana makoma wanda shi ne mafi hatsari a tsawon tarihinta.”
Har ila yau Haykal ya ce; ‘Yanto da dukkanin kasar daga mamaya ne zai sa samun ‘yancin kasar ya cika.