UNICEF: Akalla yara 28 ne ke mutuwa a kowace rana a Gaza sakamakon harin Isra’ila da yunwa

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fada a ranar Litinin cewa kimanin yara 28 ne ake kashewa a kullum a

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fada a ranar Litinin cewa kimanin yara 28 ne ake kashewa a kullum a zirin Gaza sakamakon harin bama-baman Isra’ila da kuma yunwar da ta jefa a l’ummar yankin a ciki.

Kungiyar ta yi bayanin a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, yaran Gaza na fuskantar kisa “sakamakon tashin bama-bamai, rashin abinci mai gina jiki, yunwa, da kuma rashin muhimman kayan agaji da ayyukan kiwon lafiya.

UNICEF ta jaddada cewa yara a Gaza na bukatar abinci, ruwa, magunguna, da kuma kariya. Mafi mahimmanci kuma shi ne, suna bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa.”

A wani labarin kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa, sama da mutane 1,500 ne aka kashe a zirin Gaza tun a watan Mayun da ya gabata, a lokacin da suke kokarin samun abinci, a hare-haren da Isra’ila ta ke kaiwa a wuraren da ake yin amfani da su wajen rarraba kayan agaji, ko kuma ta hanyar kai harin a kan ayarin motocin Majalisar Dinkin Duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments