Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe

Majiyar ‘yan hamayyar siyasar kasar Uganda sun sanar da cewa, jami’an tsaron kasar sun kama magoya bayan Bobi Wine dake takarar shugabancin kasar 300 a

Majiyar ‘yan hamayyar siyasar kasar Uganda sun sanar da cewa, jami’an tsaron kasar sun kama magoya bayan Bobi Wine dake takarar shugabancin kasar 300 a tsawon yakin neman zabe.

Mai magana da yawun Bobi Wine dan takarar shugabancin kasar ya fada a jiya Talata cewa; jami’an tsaron kasar sun kama fiye da mutane 300 da suke goyon bayansa tun da aka fara yakin neman zabe daga watan Janairu zuwa yanzu.

Bob Wine wanda shahararren mawaki ne ya juye zuwa dan siyasa, yana yin takara a karo na biyu da shugaban kasar mai ci, Uweri Musaveni. A zaben 2021 Bob Wine wanda sunansa na yanke shi ne Robert Kyagulanyi,, ya zo na biyu.

Kakakin jam’iyyarsa ta NUP,ya ce, a cikin wannan makon ma an kama mutane da dama, kuma ana tsare da su ne a cikin babban birnin kasar Kamfala.

Majiyar jam’iyyar hamayyar ta kuma ce, a ranar Litinin da aka bude yakin neman zabe kadai na kame mutane sun kai 100, sai kuma wani adadi mai yawa a jiya Talata.

Jami’an tsaron kasar sun sanar da kame mutane 7 bayan da su ka yi jefe-jefe da duwatsu a lokacin yakin neman zabe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted