Tutocin Falasdinu Sun Yi Ta Kadawa A Birnin Sao Paulo Na kasar Brazil, A Gagarumin Gaggami Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa Suka Shirya

Masu rajin kare hakkin bil’adama a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, sun ratsa tsakiyar birnin tare da makeken tutar kasar Falasdinu inda suke kira

Masu rajin kare hakkin bil’adama a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, sun ratsa tsakiyar birnin tare da makeken tutar kasar Falasdinu inda suke kira zuwa ga cikekken yenci ga Falasdinawa da kuma dakatar da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a can.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, a dai dai lokacinda ake kira zuwa ga goyin bayan mutanen gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashi a fagen kasa da kasa, mutanen Brazil sun fito kwansu da kwarkwartansu a birnin Sao Paulo don tabbatar da wannan kiran.

A halin yanzu dai ana kokarin samarda kawance ta kasa da kasa, wacce zata game ko ina a duniya, don goyon bayan mutanen Falasdinu da kuma korar yahudawa yan mulkin mallaka kuma yan mamaya, daga kasar Falasdinu da aka mamaye.

Labarin ya kara da cewa, wadanda suka yi jawabi a gaggamin taron na Sao Paulo sun bukaci a kawo karshen kissan kiyashi a Gaza, a kuma kafa kasar Falasdinu mai cikekken yenci daga teku zuwa kogi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments