Turkiyya : Mu Muka Bukaci Iran Da Rasha Da Ka Da Su Dauki Mataki A Lokacin Farmakin ‘Yan Tawayen Siriya

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya yi ikirarin cewa, Turkiyya ta yi nasarar shawo kan Iran da Rasha da kada su tsoma baki ta hanyar soji

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya yi ikirarin cewa, Turkiyya ta yi nasarar shawo kan Iran da Rasha da kada su tsoma baki ta hanyar soji a lokacin farmakin da ‘yan tawayen Siriya suka kai wanda ya kai ga kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a ranar 8 ga watan Disamba.

A wata hira da ya yi da tashar NTV ta Turkiyya a baya-bayan nan, Hakan Fidan ya bayyana cewa: “Abu mafi mahimmanci da ya kamata mu yi shi ne tattaunawa da Rasha da Iran don tabbatar da cewa ba za su amfani da karfin soji ba, lokacin da ‘yan tawaye ke dannawa ba, kuma sun fahimci lamarin.”

Sabbin bayanai da kafar yada labarai ta Tehran Times ta samu sun nuna cewa taron kolin na ranar 7 ga watan Disamba a karkashin dandalin Astana, ya nuna cewa Turkiyya ta amince da wani tsarin da zai ba da damar yin shawarwari kai tsaye tsakanin shugaban kasar Siriya da dakarun ‘yan tawaye.

Wata majiya mai ruwa da tsaki a tattaunawar ta Doha ta shaidawa Tehran Times cewa: “An amince da cewa, za a warware rikicin Siriya ta hanyar siyasa, inda gwamnatin Assad da ‘yan adawa masu dauke da makamai suka shiga tattaunawa.

To saidai wasu bayanai sun ce, abubuwan da suka faru a Siriya, sun nuna cewa Turkiyya ba ta bi abin da ta sanya wa hannu ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments