Turkiya: Fiye Da’Yan Adawa 300,000 Su Ka Yi Zanga-Zanga Nuna Kin Jinin  Erdogan

Kamfanin dillancin labarun “al-Somariyya News” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda

Kamfanin dillancin labarun “al-Somariyya News” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda su ka fito Zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Rajab Tayyib Urdugan sakamakon sauke da kama ‘yan hamayyar siyasa da ya yi daga kan mukamansu da su ka hada da magajin garin birnin  Istanbulm ya kai 300,000.

Magajin garin Istanbul Imam Uglu ya yi watsi da duk wata tuhuma da aka yi masa ta hannu a cin hanci da rashawa.

Kamfanin dillancin labaran “Reuters” ya nakalto wata majiyar shari’a tana cewa Imam Uglu ya yi watsi da dukkanin thume-tuhumen da aka yi masa masu alaka a cin hanci da rashawa.

Shi dai Imam Uglu zai tsaya takarar shugabancin kasa da Urdugan, kuma ana tsinkayo cewa zai iya lashe zabe.

Jami’iyyar adawa da Imam Uglu ya fito daga cikinta “ Turkish Republican Party” ta yi Allawadai da kama Imam Uglu, tare da bayyana shi da cewa, bi ta da kulli ne na siyasa kawai.

Bayan kama Imam Uuglu Zanga-zanga ta barke a cikin birane da garuruwa mabanbanta na kasar ta Turkiya  tare da yin tir da abinda ya faru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments