Rahotanni sun ambaci cewa bayan ficewar sojan Faransa na karshe daga sansanin Abaci dake gabacin kasar Chadi,kasar Turkiya tana shirin maye gurbinta.
Wata majiyar kasar Turkiya ta shaidawa wata kafar labaru ta Afirka cewa, Ankara tana shirin girke jiragen yaki marasa matuki a cikin sansanin dake kan iyaka da kasar Libya akokarin da take yi na cike gurbin da Faransa ta bari, da zummar tabbatar da kanta a cikin wanann yankin na Afirka.
Gwamnatin Chadi ta bai wa Turkiya sansanin na Abaci a karkashin yarjejeniyar da kasashen biyu su ka cimmawa a tsakiyar watan da ya gabata,bayan doguwar tattaunawa da aka yi a tsakanin jami’an gwmanatocin kasashen biyu.
Haka nan kuma rahoton ya ce, kasar Turkiya ta bai wa gwamnatin kasar ta Chadi jiragen sama marasa matuki samfurin Beyraghdar. Haka nan kuma da akwai masu bayar da shawara na soja da dama daga kasar ta Turkiya a cikin kasar ta Chadi.