Turkiya Ta Fitar Da Sammacin Kama Natanyaho Da Wasu Jami’ian Isra’ila Kan Yakin Gaza

Rahotanni sun bayyana cewa a kasar Turkiya an fitar da hukumci kama prime ministan Isra’ila banjamin Natanyaho da wasu jami’an Isra’ila guda 37 da laifin

Rahotanni sun bayyana cewa a kasar Turkiya an fitar da hukumci kama prime ministan Isra’ila banjamin Natanyaho da wasu jami’an Isra’ila guda 37 da laifin keta hakkin bil adama da kuma yin kisan kare dangi kan alummar Gaza a lokacin yaki,

Wannan yana nuna irin mataki mai tsauri na doka da aka dauka kan jami’an Isra’ila a baya bayan nan, kan laifuka yaki da suka tafka kan bil adam a yakin Gaza, da kuma karfafa kasashen duniya daukar matakin da ya dace kan zargin da ake mata na kai hare-haren kan fararen hula.

Sabanin tsakanin Ankara da tel aviv ya kara tsananta ne tun bayan da ta fara kai hare-haren kan fararen hula a yankin gaza a shekara ta 2023 , inda turkiya ta yi tir da isra’aila tare da bayyana shi a matsayin harin ta’adanci,

kuma tabi sahun kasar Afrika ta kudu wajen shigar da Isra’ila kara kan zargin kisan kare dangi a gaban kotun duniya ta ICJ, Jami’an Isra’ila guda 37 ne aka ambaci sunansu na wadanda aka bada Izinin kamasu, sai dai ba’a fallasa sunayensu duka ba ga bayyanar jama’a ,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments