Tsohon shugaban hukumar leken asirin Saudiyya, Yarima Turki Al-Faisal, ya yi furuci da cewa: Amurka ta tattauna da kasar Saudiyya kan yadda musamman za a kyautata alaka tsakanin Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila.
A tattaunawar da ya gudanar a yayin zaman taron karawa juna sani da cibiyar kula da huldar kasa da kasa ta Royal Chatham House ta shirya birnin Landan na kasar Birtaniya Al-Faisal ya ce: Saudiyya na tattaunawa da Amurka game da batun neman kyautata alaka tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma Saudiyya ta gindaya sharadin cewa idan har zata kyautata alakarta da haramtacciyar kasar Isra’ila sai an kai ga kafa yantacciyar kasar Falasdinu to daga nan ne zata fara yunkurin kyautata alakarta da haramtacciyar kasar ta Isra’ila.
Haka nan Al-Faisal ya yi nuni da yadda yahudawan sahayoniyya suke aiwatar da kisan kiyashin kan Falasdinawa, ba kawai a Gaza kadai ba, har ma da yankin gabar yammacin kogin Jordan.
A halin yanzu haka dai Al-Faisal baya rike da wani mukami a hukumance a kasar Saudiyya, amma ya bayyana tunanin Saudiyya game da Falasdinu da abin da ya shafe ta, dangane da ci gaba da fuskantar munanan hare-haren daga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila musamman kan Gaza.