Tsohon ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ba da umarnin sojojinsu su kashe fursunoni yahudawa da masu tsaronsu a Gaza
Tsohon Ministan tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da aka kora Yoav Gallant a jiya Alhamis ya yi bayani kan matakan da sojojin mamayar Isra’ila suka dauka na tunkarar fursunonin yahudawan sahayoniyya da masu garkuwa da su a Zirin Gaza.
A cewar shafin Falestine Today, Gallant ya ce: “Sun ba wa sojojin mamayar Isra’ila umarnin yin amfani da hanyar Hannibal, wato kashe fursunoni ‘yan uwansu da aka yi garkuwa da su tare da masu garkuwa da su a Gaza.”
Ya kara da cewa: A jajiberin fara kai farmaki ta kasa kan Gaza, fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gaya masa abubuwa biyu cewa: Za a kashe dubban sojojin yahudawan sahayoniyya a Gaza, kuma kungiyar Hamas za ta yi amfani da fursunonin yahudawan sahayoniyya da take tsare da su a matsayin garkuwa don haka a kashe su duka.