Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar Chadi kuma tsohon fira ministan kasar Succès Masra ya zargi kasar Faransa da cewa tana yi wa tsarin demokradiyyar kasar kafar angulu.
Shugaban ‘yan hamayyar siyasar na kasar Chadi ya kuma ce; Zai kauracewa shiga zaben da za a yi a nan gaba a ranar 29 ga watan Disamba mai zuwa.
Succes Masra ya kuma ce a bayan fage Faransa tana goyon bayan iyalan shugaba Muhammad Idris, tare da yin watsi da wanene zabin al’ummar kasar ta Chadi.
Tsohon Fira ministan na kasar Chadi ya kuma ce; A yanayi irin wannan babu abinda ya fi dacewa sai zama dan ba-ruwanmu, amma dai a fili yake cewa Faransa tana fifita wasu iyalai guda akan sauran al’ummar kasar ta Chadi da take son samar da sauyi.
Shi dai jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Chadi ya yi azamar kauracewa zaben ‘yan majalisa da kuma na magattan gari da za a yi a ranar 29 ga watan Disamba mai zuwa.
Shi kuwa shugaban kasar mai ci Muhammad Idris Deby ya hau karagar mulki ne a ranar 6 ga watan Yulin da ya wuce, wanda kungiyoyin da suke sa ido na waje su ka ce, ba a yi zaben cikin ‘yanci ba.