Trump Yayi Barazanar Karawa Kasar Rasha Takunkuman Tattalin Arziki Idan Taki Kawo Karshen Yaki A Ukraine

Sabon shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi barazanar karawa kayakin Rasha da suke shigowa kasar haraji, ko kudin fito sannan ta karawa kasar takunkuman tattalin

Sabon shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi barazanar karawa kayakin Rasha da suke shigowa kasar haraji, ko kudin fito sannan ta karawa kasar takunkuman tattalin arziki, idan taki amincewa da yarjeniyar sulhu da kasar Ukraine.

Tashar talabijan ta Presstv, a nan Tehran ta nakalto shugaban ya na cewa: Idan kasar Rasha ta ki ta kawo karshen yakin na Ukraine, to bai da zabi in banda kara dora mata takunkuman tattalin arziki. Da kuma kara haraji wa kayakin da suke shigowa kasar Amurka daga Rasah.

Trump ya kara da cewa, ya na girmama shugaban kasar Rasha Vladimar Putin, saboda halaye masu kyau da yake da su, amma ya tattauna da shugaban kasar Ukraine, Vlodomir Zeleski wanda ya fada masa cewa a shirye yake a kawo karshen yaki da Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments