Fadar mulkin Amurka “White House” ta ba da sanarwan cewa shugaba Donal Trump ya soke cire kasar Cuba daga cikin jerin kasashen da Amurka ta dauka a matsayin masu tallafawa ayyukan ta’addanci.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar fadar white House a ranar Litinin, tana cewa wannan matakin zai kara rikicin da ke tsakanin kasashen biyu na kimanin shekaru 60 da suka gabata.
Shugaban Biden dai ya yi kokarin sassautawa kasar ta Cuba takunkuman tattalin arziki da kuma matsin lamban da takewa kasar ta cuba tun lokacin yakin cacan baki. Sabon matakin na Shugaba Trump ya sake mayar da al’amurra baya a alakar kasashen biyu.
A ranar 14 ga watan Janairu ne tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya soke dokar sanya Cuba cikin Jerin kasashen wadanda Amurka ta dauka a matsayin masu tallafawa ayyukan ta’addanci.
A ranar da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa Trump ya soke dokokin tsohuwar gwamnatiun har guda 78.
Kafin haka dai Obama ma ya soke wannan dokar a shekara ta 2015, amma Trump ya sake maida ita, sannan Biden ya soke, yanzu kuma Trump din ya sake maida ita a karo na biyu.