Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine.
Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta na Ukraine.
Wannan labarin ya Eu ta kira taron gaggawa don tattauna wannan batun. Sannan Sir Keir Starmer ya kuma hanya zuwa Amurka da gaggawa.
Mataimakin shugaban kuma yakadansa na musamman a kan shirin tsagaita wuta a Ukraine ya bayyanawa Ukrain kan cewa batun shigar Ukraine kungiyar tsaro da NATO bai da wani muhimmanci a wajen shugaba Trump a yanzu.
Mr Vances ya bayyana hakane a taron tsaro da ke gudana a birnin Munich.