Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, Amurka ta na son mallakar ma’adanan na kasar Ukiraniya, wadadensu ya kudadensu ya kai dalar Amurka biliyan 500, a matsayin mayar da kwaryar taimakon Amurkan ta fuskar soja da makamai.
A wata hira da tashar talabijin ta “FOX NEWS” ta yi da shi, shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya ce, ya na son Amurka ta mallaki ma’anadai na kasar Ukiraniya a matsayin ladar da tallafin sojen da take bukata daga Amurka.
Gwamnatin Donald Trump ta gabatar wa da Kiev shawarar yin musayar ma’adanai na musamman da irinsu sun yi karanci a duniya, da take da su, na kaso 50% da hakan zai zama abinda take biyan Amurka da su, madadin taimakon soje da take samu daga wajenta.
Sakataren Biatul-Malin Amurka Scott Bessent ne, ya gabatarwa da shugaban kasar Ukiraniya Volodymir Zeleski shawarar hakan a wata ganawa da su ka yi a ranar Larabar da ta gabata a birkin Kiev.
A karkashin wannan shawarar Amurkan za ta aike da sojojinta domin bada kariya ga wuraren hako wadannan ma’adanan a gabashin turai.
Tashar talabijin ta NBC da ta watsa wannan labarin ta kuma ambato cewa, shugaban kasar ta Ukiraniya ya ki rattaba hannu akan yarjejeniyar ya kara da cewa, zai tuntubi jami’an gwamnatin kasar sa kafin haka.