Trump Ya Bai Wa Tarayyar Turai Zabi Tsakanin Sayen Makamashi Daga Amurka Ko Kuma Ya Dora Musu  Kudaden Fito Masu yawa

Jaridar Financial Times ta Birtaniya ta buga labarin dake cewa: Zababben shugaban kasar ta Amurka Donald Trump Ya zama wajibi ga kasashen tarayyar turai su 

Jaridar Financial Times ta Birtaniya ta buga labarin dake cewa: Zababben shugaban kasar ta Amurka Donald Trump Ya zama wajibi ga kasashen tarayyar turai su  rika sayen man fetur da iskar gas masu yawa daga Amurkan, ko kuma ya kakaba musu  kudaden fito masu yawa akan kayan da suke shigar da shi Amurka.

Trump ya rubuta a haifnsa na “Trus Social” cewa na fada wa tarayyar turai cewa wajibi ne su cika gibin dake tsakanin su da Amurka ta hanyar sayen man fetur dinmu mai tarin yawa da kuma iskar gas dinmu, ko kuma su fuskanci  Karin kudaden fito masu yawa da zai zama shi kadai ne mafita.

Wannan matakin na Trump ya zo ne dai bayan da kasashen turai din su samar da cewa sun gabatar da shirinsu na sayen makamashi daga Amurka.

Shugabar tarayyar turai din Ursula von der Leyen ta fada a cikin watan Nuwamba cewa; Tarayyar turai za ta yi tunanin sayen makamashi mai yawa daga Amurka.

Ta kara da cewa, har yanzu muna cigaba da sayen iskar gas mai yawa daga kasar Rasha, saboda me ba za mu maye gurbinsa da na Amurka ba wanda ya fi sauki a wurinmu?

Wani jami’in tarayyar turai ya bayyana abinda Trump din ya fada da cewa, baraza ce , domin tun tuni Ursula von der Leyen ta ce za su rika sayen makamashin daga Amurka.

Jaridar ta Birtaniya ta kuma ce, Trump din  ya kuma yi barazanar kara kudaden fito akan  kasar China da kaso 20%.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments