Trump:  Shugabanin Hamas ba su da hannu a kisan sojojin Isra’ila 2 a Gaza

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shugabannin Hamas ba su da hannu a harin da aka kaiwa sojojin Isra’ila a kudancin Gaza. Da yake magana

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shugabannin Hamas ba su da hannu a harin da aka kaiwa sojojin Isra’ila a kudancin Gaza.

Da yake magana da jami’an sojin sama na Amurka wato Air Force One a jiya Lahadi 19 ga Oktoba, Trump ya danganta harin da wasu da ya kira wadanda suka yi tawaye a cikin kungiyar Hamas.

Trump ya bayyana a fili cewa: Ko ta yaya dai, za a kula da lamarin yadda ya kamata. Za a dauki matakai masu tsauri, amma yadda ya kamata a cewarsa.

Trump ya kuma kara da cewa, yana fatan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza za ta ci gaba da tabbatar da manufofin Washington na wanzar da zaman lafiya a Gaza.

An kashe sojojin Isra’ila biyu a  jiya Lahadi a kudancin zirin Gaza, kamar yadda rundunar sojin mamaya ta tabbatar. Sojojin biyu an bayyana makamansu da Manjo da kuma Sajan Staff, dukkansu ‘yan sassan sojojin yahudawan da ke aiki a kudancin kasar ne.

Wannan farmakin ya zo ne a daidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yankuna daban-daban na zirin Gaza, musamman a kudancin yankin, inda sojojin Isra’ila suke ci gaba da killace yankin tare da ci gaba da rufe mashigar Rafah, da kuma hana shigar da kayan agaji zuwa ga al’ummar Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted