Shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas cewa zai ba da izinin sake kai sabbin hare-hare a zirin Gaza muddin kungiyar bat a saki sauran Isra’ilawan da ta yi garkuwa da sub a.
Barazanar ta Trump ta zo ne a wata tattaunawa kai tsaye a Doha tsakanin wakilinsa kan al’amuran da suka shafi fursunonin, Adam Boehler, da shugabannin Hamas, a yunkurin cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni a Gaza.
Trump ya ambaci haka ne bayan ganawa da fursunoni shida da aka sako a wani bangare na matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Wani babban kusa na kungiyar Hamas ya shaidawa Al Mayadeen cewa, taron na baya-bayan nan ya bar wa bangaren Amurka kyakkyawar fahimta dangane da yiwuwar tattaunawa da kungiyar.
Sai dai jami’in ya bayyana cewa, wakilin na Amurka ya mayar da hankali ne kawai kan yuwuwar musayar fursunoni, kuma bai yi magana kan manyan batutuwa ba, kamar tsagaita bude wuta ko kuma kawo karshen yakin Gaza.
Ya ce “Bangaren Amurka ba su gabatar da takamaiman tsari na musayar fursunoni ba amma sun saurari ra’ayin Hamas kan lamarin.”
Ya kara da cewa, taron ya gudana ne bisa bukatar Amurka kuma ya ba wa jami’an Isra’ila mamaki matuka.