Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya.
Shugaban na kasar Amurka ya kara da cewa; Volodymyr Zelenskyy ya sa Amurka ta kashe dala biliyan 350 da ya shiga cikin yakin da ba zai iya samun nasara ba.
Har ila yau, shugaban na Amurka ya ce, shi kanshi Volodymyr Zelenskyy ya yi furuci da cewa, rabin kudaden da mu ka aika masa sun bace, kuma ya ki gudanar da yin zabe, don haka masu goyon bayansa ‘yan kadan ne.”
Bugu da kari Trump ya ce, ko kadan bai kamata a ce yaki ya barke ba, domin yaki ne da babu yadda za a yi ya yi nasara ba tare da goyon bayan Amurka da kuma Trump ba, yana mai yin ishara da cewa, ahalin yanzu Amurka tana tattaunawa cikin nasara da Rasha domin kawo karshen yakin.”
Wani sashe na sakon Trump din ya kunshi cewa; Ina son kasar Ukiraniya, sai dai abinda Volodymyr Zelenskyy ya yi, ya munana, ya ruguza kasarsa, kuma miliyoyin mutane sun mutu ba tare da dalili ba.
A gefe daya, kasashen turai sun mayar da martani akan maganganun na Trump, inda shugaban gwamantin Jamus ya ce shugaban kasar ta Ukiraniya ba dan dan kama-karya ba ne.