Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza

Masar za ta shirya wani taron kasa da kasa kan zaman lafiya a birnin Sharm el-Sheikh da ke bakin Tekun Maliya a ranar Litinin, wanda

Masar za ta shirya wani taron kasa da kasa kan zaman lafiya a birnin Sharm el-Sheikh da ke bakin Tekun Maliya a ranar Litinin, wanda Shugaba Abdel Fattah el-Sisi da takwaransa na Amurka, Donald Trump, za su jagoranta.  

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta bayyana cewa taron zai tattaro shugabanni daga kasashe fiye da 20.

Manufar taron ita ce “kawo karshen yakin Gaza, da karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya, da kuma fara wani sabon mataki na tsaro da kwanciyar hankali a yankin,” in ji sanarwar.

A ranar Laraba Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da mataki na farko na wani shiri mai matakai 20 da ya gabatar a ranar 29 ga Satumba don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da sakin dukkan fursunonin Isra’ila da ke hannun Hamas a musayar fursunoni Falasdinawa kusan 2,000, da kuma janye sojojin Isra’ila daga dukkan yankin Gaza.

Mataki na biyu na shirin ya tanadi kafa sabon tsarin mulki a Gaza, samar da wata rundunar tsaro da za ta kunshi Falasdinawa da sojoji daga kasashen Larabawa da Musulmi, da kuma kwace makamai daga hannun Hamas.

Tun daga watan Oktoba na 2023, hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa fiye da 67,600 a Gaza, yawancinsu mata da yara, tare da mayar da yankin kufai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted