Matakatin shugaban Amurka Donald Trump na nada tsohon fira ministan birtaniya Tony Blair a matsayin mai ruwa da tsaki cikin alamuran gaza bayan dakatar da bude wuta ya fuskancin turjiya daga kasashen larabawa da kuma na musulmi, Balair shi ne mutum daya da aka ayyana sunansa daga cikin mambobin kwamitin tabbatar da sulhu da trump ya bada shawara na sanya ido bayan kawo karshen yaki tsakanin bangarorin biyu.
Akwai damuwa sosai da shakku kan kasancewar Blair daga cikin masu ruwa da tsaki a alamuran yankin, musamman bayan goyon bayan da ya nuna wajen kai wa iraki hari tare da tsohon shugaban Amurka na wancan lokacin a shekara ta 2003 ,a gefe daya kuma yana kare Isra’ila, jamai’an diplomasiyan larabawa sun nuna damuwa sosai inda suke ganin shigar da blair cikin lamarin zai raunana matsayin falasdinu, kuma zai kara dagula kokarin samar da zaman lafiya a Gaza,
Jami’an diplomasiyar kasashen larabawa 3 sun bayyana wa jaridar financial times cewa nada blair da aka yi ya dauki hankali sosai, da kuma yadda aka ajiye falasdinawa a gefe, ana son sake dawo da wani nau’in mulkin mallaka ta wani sabon salo,
Wasu kasashen larabawa da na musulmi ciki har da Saudi arebiya, masar, jodan, turkiya da kuma kasar Indonesia an tuntubesu game da shirin kuma ana fatan za su bada gudunmawar dakaru da kuma shirin sake gina yankin gaza , sai dai dama daga cikinsu suna ci gaba da nuna shakku kan mambobin kwamitin zaman lafiya musamman kasancewar blair a ciki, da suke ganin haka zai kawo cikas wajen aiwatar da shirin.